Hukumar da ke sanya idanu kan harkokin man fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta sanar da cewa sabuwar matatar mai ta Dangote za ta fara samar da lita miliyan 25 na man fetur a kowace rana ga kasuwannin Nijeriya a cikin watan Satumbar da muke ciki.
Ana sa ran adadin man zai ƙaru zuwa lita miliyan 30 a kowace rana daga watan Oktoba.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin sada zumuntarta na X ta bayyana cewa, a wani taro da suka yi a Abuja ranar Talata, NMDPRA da Kamfanin NNPCL sun amince da fara sayar da ɗanyen mai ga matatar Dangote da kuɗin ƙasar wato Naira.
Bayan shafe sama da shekara guda da taƙaddamar da aikinta a watan Mayun 2023, matatar Dangote, a ranar Talata, ta fara fitar da man fetur ɗin.
A jiya ne dai kamfanin NNPCL ta ƙara farashin man fetur daga naira 617 zuwa naira 897.
Aliko Dangote ya ce da zarar kamfaninsa ya kammala shirye-shirye da NNPCL, man fetur na kamfanin zai shiga kasuwa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 20 hours 31 minutes 45 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 22 hours 13 minutes 10 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com