Tun bayan sanar da karin farashin man fetur a kasar dake yammacin Afirka Al’umma suka shiga zulumi da tsammanin ko wanne mataki kungiyoyin kwadagon kasazr zasu dauka kan wannan mataki na Kamfanin NNPCL na karin.
ko da yake dai haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago a kasar ta Nigeria Labour Congress (NLC) ta zargi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da karya yarjejeniyar da suka ƙulla kafin sanar da ƙarin farashin man fetur ranar Talata.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a yammacin yau Talata ta ce ɗaya daga cikin dalilan da suka sa suka amince da naira 70,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi a watan Yuli shi ne ba za a ƙara kuɗin fetur ba.
“Muna sane da zaɓin da shugaban ƙasa ya ba mu cewa ko dai a ba mu N250,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi (amma a ƙara farashin fetur zuwa N1,500 ko N2,000) ko kuma N70,000 (a bar farashin yadda yake),” a cewar NLC.
“Mun zaɓi na biyun saboda ba za mu juri a cigaba da azabtar da ‘yan Najeriya ba. Amma yanzu ga shi ko sabon albashin ba a fara biya ba an sake zuwa mana da abin da ba za mu iya fahimta ba.”
Ƙungiyar ta bayyana ƙarin a matsayin “abin takaici” kuma “mai banhaushi”.
Da safiyar talata ne dai kamfanin mai na NNPCL na gwamnatin Najeriya ya sanar da sauya farashin daga N617 zuwa N897 kan kowace lita, abin da ya sa ‘yan Najeriya da dama suka nuna ɓacin ransu.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 18 minutes 55 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 20 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com