Home General Gwamnatin Nijeriya ta bar Jakki tana Tukan Taiki – Atiku

Gwamnatin Nijeriya ta bar Jakki tana Tukan Taiki – Atiku

Tsohon mataimakain shugaban kasa kuma Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin ƙasar da mayar da hankali kan wasu abubuwa da ya kira marasa muhimmanci tare da yin watsi da matsala tsaro da ƙasar ke fama da ita.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon ɗan takarar shugaba ƙasar na jam’iyyar PDP ya yi Allah wadai da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai jihar Yobe, da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Ya kuma yi tsokaci kan yawan tashe-tashen hankula da ke ci gaba da faruwa a jihohin Katsina da Sokoto da sauran sassan Arewa.

Atiku ya zargi gwamnati da cewa ta fi damuwa da kama masu zanga-zanga, maimakon magance matsalar rashin tsaro.

“Duk da mummunan zubar da jini da aka yi a Yobe, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, da kuma ɓarnar da aka yi a ƙauyuka da dama a Katsina da Sakoto, da sauran garuruwan da ke yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, da dukkan alamu gwamnati ta fi mayar da hankali kan ayyukanta da sauran abubuwa da ba zu da muhimmanci.” in ji Atiku.

Atiku ya kuma yi nuni da tashe-tashen hankulan da ‘yan Boko Haram ke haifarwa da rigingimun siyasa a kudu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp