Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin Abuja ta dakatar da hukumar zaben jihar Kano (KANSIEC) karbar kudin sayen form na naira miliyan goma da miliyan biyar ga ‘yan takarkarun dake zawarcin kujerun shugabancin kananan hukumomi da mazabu a jihar a zaben kananan hukumomin dake tafe na wucin gadi.
Da yake bayar da umarnin mai shari’a Emeka Nwite a ranar laraba, bisa karara da jam’iyyun Action Peoples Party (APP), Action Democratic Party (ADP), da Social Democratic Party (SDP), suka shigar da hukumar zaben jihar ta KANSIEC gaban kotun.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Idan dai za’a iya tunawa hukumar zaben ta saka kudin sayen naira miliyan 10 ga dukkan dan takarar dake da muradin tsayawa takarar shugabancin karamar hukuma, haka kuma naira miliyan biyar ga dukkan wanda ke zawarcin kujera a mazaba wato kansila.
Haka kuma hukumar ta sake yin mi’ara koma baya kan ranar zaben da ta sanya tun da fari na 26 ga watan Oktoba, in ta dawo da ita ba zuwa 30 ga watan Nuwamba shekarar 2024.
A Nijeriya dai ana kallon gwamnonin jihohin kasar na tururuwar gudanar da zaben kananan hukumomi ne bisa umarnin kotun kolin kasar na tabbatarwa da kananan hukumomin cin gashin kai.
PRNigeria Hausa












