Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce man fetur da kansa ne zai nemawa kansa farashi a kasuwa.
A wata tattaunawa da aka yi da mataimakin shugaban kamfanin na ƙasa Mista Adedapo Segun, ya ce kundin tsarin mulki bai ƙayyade waɗanda za su tsayar da farashin man fetur ba.
A cewarsa, sashe na 205 da ya kafa kamfanin, ya bashi damar sakin fetur don nemawa kansa farashi a kasuwa.
Read Also:
Ya ƙara da cewa dangane da tsadarsa da mutane ke kokawa, batu ne da ya shafi chanjin kuɗaɗe.
Amma ya ce su na ƙoƙarin su da dilallan man na ƙasa don ganin an magance karancinsa.
Kuma ya sake tabbatarwa da ƴan Najeriya cewar, nan da kwanaki kadan za a kawo ƙarshen matsalar ƙarancin man baki ɗaya.
A cewar kamfanin, a halin yanzu man fetur na nemawa kansa farashi ne a kasuwa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 15 minutes 15 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 56 minutes 40 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com