Wani faifen Bidiyo da yayi ta yawo a kafafen internet da kafafen sada zumunta, musamman manhajar WhatsApp da shafin Facebook, wanda ta nuna wasu tarin mutane masu zanga-zanga sun yi wa fadar sarkin musulmi da ke sokoto tsinke in da suke bukatar sauyin gwamnatin idan wakilan gwamnatin tarayya sun kai ziyara jihar.
An rubuta cewa: “Sokoto a ya! Yadda ma su zanga-zanga suka taro a fadar Sarkin Musulmi, suna ihun “ ba ma Tinubu…. Sai Obi ko kuma Sojoji su karbi kasar.”
To amma, tawagar binciken sahihancin labarai ta PRNigeria ta bi diddigin asalin bidiyon da ake ikirari a kai, wadda aka wallafa a shafukan sada zumuntar da suka hadar da Facebook, bayan da karamin minstan tsaron Nijeriya Bello Matawalle ya jagorancin tawagar manyan sojoji zuwa Sokoto, domin duba ayyukan sojojin na kawar da matsalar rashin tsaro da ta addabi shiyyar Arewa maso yammacin Nijeriya.
Read Also:
haka kuma, wani bincike da aka fadada ya tabbatar da cewa bidiyon tsoho ne da aka dauka lokacin zanga –zangar ‘EndBadGovernance’, wadda ta gudana a watan Agustan 2024, akalla wata guda bayan ikirarin.
Zanga-zangar #EndBadGovernance, wadda aka fi sani da #EndbadGovernanceInNigeria ta kunshi jerin zanga-zangar da babu wadanda suka shirya ta wadanda suka gudana a mabanbanta wurare a fadin Nijeriya da ka gudanar a 1 ga watan Agustan 2024 zuwa 10 ga watan. Wannan zanga-zanga ta faru ne sakamakon tsadar kayan masarufi a fadin kasar abin da ya haifar da tsadar rayuwa da wahalhalun rayuwa ga al’ummar kasar.
KAMMALAWA: binciken da jaridar PRNigeria ta gudanar ya tabbatar da wannan bidiyon da aka yada aka ce masu zanga-zanga ne a fadar sarkin musulmi da ke Sokoto lokacin da tawagar karamin ministan Tsaron Nijeriya da shuwagabannin tsaron kasar suka ziyarci fadar, gaskiya tsohon bidiyo ne na zanga-zangar EndBadGovernance da aka gudanar a watan Agustan 2024.
Don haka, PRNigeria ta yanke hukuncin kan ikirarin da ake da ke cewa masu zanga-zanga a fadar mai Alfarma sakin musulmi da ke jihar Sokoto, da ke nuna goyon bayan Peter Obi ko sauya gwamnati labarin karya ne.
By PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1462 days 9 hours 25 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1444 days 11 hours 6 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com