SERAP ta buƙaci Tinubu ya tilasta wa NNPCL janye ƙarin kuɗin man fetur

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi amfani da ”matsayinsa ya tilasta wa babban kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya gaggauta janye ƙarin farashin man fetur da ƙungiyar ta kira ‘wanda ya saɓa wa doka’.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi ta ce ƙarin kuɗin man fetur ɗin ya saɓa wa kundin tsarin mulki tare da dokokin ƙasar game da kare haƙƙin bil-adama.

SERAP ta kuma buƙaci shugaba Tinubu ya ”umarci babban lauyan gwamnatin ƙasar, Lateef Fagbemi, SAN da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su binciki zarge-zargen cin hanci da almabazzaranci a ake yi wa kamfanin NNPCL.

Ciki har da kuɗin tallafin ƙwatar kai (bailout), na dala miliyan 300 da kamfanin ya karɓa daga gwamnatin tarayya a watan Agustan da ya gabata, da kuma zargin kamfanin da rashin saka ribar mai a asusun gwamnati.

SERAP ta ce “ya kamata a gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifi a NNPCL a gaban kotu domin su fuskanci hukunci, idan har an same su da laifi, tare da ƙwato duk abin da suka sata”.

ƙungiyar ta kara da cewa cin hanci da rashawa da ake zargin samu fannin man fetur da kuma kashe kuɗin gwamnati ba bisa ƙai’da ba, da kuma yin ƙunbiya-ƙunbiya ko rufa-rufa sun taimaka wajen ƙarin taɓarɓarewar al’amura a kamfanin, wanda kuma shi ke haifar da ƙarin kuɗin man fetur a koyaushe a ƙasar.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 15 hours 3 minutes 48 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 45 minutes 13 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com