Wata mummunar ambaliyar ruwa ta raba mutane sama da 1,000 da muhallansu tare da hallaka yara biyu a Kafanchan da ke cikin ƙaramar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.
Misis Christy Usman, mataimakiyar shugabar ƙaramar hukumar Jema’a ce ta bayyana hakan, a wata ziyara da kwamitin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa domin nazari kan tasirin ambaliyar.
Ta ce ambaliyar wadda ta shafi “wasu sassan garin Kafanchan da Jagindi da Atuku da Aso da kuma Bade ta lalata gonaki da dama da kuma amfanin gona da darajarsu takai miliyoyin naira.”
“Ambaliyar ta yi illa ga tattalin arzikin ƙaramar hukumar Jema’a, amma Gwamnatin jihar ta dauki mataki cikin gaggawa.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 23 hours 55 minutes 16 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 1 hour 36 minutes 41 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com