Rahotanni daga garin Maiduguri dake jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya ta tabbatar da cewa dubban mutane sun rasa matsugunansu yayin da Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali da trabiyya ta kasar ta sake kamo fursunoni uku da suka tsere bayan rugujewar kurkuku, sannan kashi 80% na dabbobin gidan zoo na Sanda Kyarimi sun mutu saboda ambaliyar ruwa mafi girma da aka samu a cikin shekaru 30 a Jihar.
Biyo bayan wannan mummunar annoba, Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi kira da a gaggauta kwashe al’ummomin da ambaliyar ta mamaye, duk da cewa baya kasar a yanzu.
Kimanin kashi 70% na birnin Maiduguri ya nutse cikin ruwa kamar yanda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana, inda ruwa ya mamaye wurare da dama, ciki har da fadar Shehun Borno, Umar Ibn Garbai El-Kanemi, ofisoshin gwamnati, da wasu manyan wurare kamar kasuwar Monday Market da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.
Read Also:
Kakakin NEMA, Manzo Ezekiel, ya bayyana cewa yankunan da aka saba ɗaukarsu a matsayin masu tudu suma sun nutse, wanda ya sa mutane da dama suka maƙale, yayin da wasu suka tashi da safe suka tarar suna cikin ruwa tsundum.
An bayyana cewa, sakamakon kwararar ruwan da ya biyo bayan fashewar Dam ɗin Alau, Maiduguri ta kasance ƙarkashin ruwa tun ƙarshen mako, inda NEMA ke ci gaba da gudanar da aikin ceto da bayar da tallafi ga mutanen da abin ya shafa.
Gwamnatin jihar ta Borno tare da haɗin gwiwar NEMA sun buɗe sansanoni guda uku don ba da mafaka ga ƴan gudun hijirar da ambaliyar ta raba da muhallansu.
Jami’an NEMA sun bayyana cewa sama da kashi 70% na mazauna Maiduguri sun rasa matsugunansu, tare da rufe makarantu da ofisoshin gwamnati sakamakon ambaliyar.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa Maiduguri don duba ɓarnar da ambaliyar ta yi, kuma ya umurci hukumomin gwamnati su hanzarta ba da taimako ga al’ummomin da abin ya shafa.
Hukumar Gidajen Gyara Hali ta Najeriya ta tabbatar da tserewar fursunoni sama da 200 daga kurkukun Maiduguri, amma a halin yanzu an sake kama uku daga cikinsu, yayin da ake ci gaba da neman sauran.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 7 hours 26 minutes 24 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 9 hours 7 minutes 49 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com