Home General Tinubu ya lashi takobin kawo karshen matsalar ambaliya a Nijeriya

Tinubu ya lashi takobin kawo karshen matsalar ambaliya a Nijeriya

NEMA
NEMA

Gwamantin tarayya Nijeriya ta lashi takobin kawo karshen ambaliyar ruwa a kasar Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana hakan ta bakin mataimakin sa Sanata Kashim Shettima a yayin da ya yi saukar gaggawa a birnin Maiduguri inda ya kai ziyarar gani-da- ido kan ambaliyar da ta rutsa da dubban mutane a garin.

Shattima ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta sa kafar wando-daya da kalubalen ambaliyar ruwa a kasar ta hanyar amfani da taswirar da za ta kawo maslaha ta dindindin.

Shettima, wanda ke jawabin cikin kaduwa a lokacin da yake tantance irin barnar da ambaliyar ta yi a garin Maiduguri, ya jajanta wa wadanda ibtila’in ya rutsa da su, inda ya bayyana musu cewa, shugaba Tinubu na tare da al’ummar da abin ya shafa, kuma gwamnatin tarayya za ta samar da dukkan abinda ake bukata domin tabbatar da tsaro da tallafawa mutanen da lamarin ya shafa.

Shettima ya danganta ambaliyar da ballewar madatsar ruwa ta Alau wanda ya ta’azzara lamarin har ya zarce irin wanda aka taba samu a baya. Sai dai kuma ya jaddada aniyarsa ta samar da mafita mai dorewa.

haka kuma ya yi kira da a ci gaba da wayar da kan al’umma kan karuwar barazanar da sauyin yanayi ke haifarwa tare da jaddada aniyar gwamnati ta magance wadannan kalubalen gaba daya.

Shettima, ya kuma yaba wa gwamnati da al’ummar jihar Borno bisa namijin kokarin da suka nuna wajen daukar matakan da suka dace akan lokaci tare da kai dauki ga al’ummar da lamarin ya shafa a cikin gaugawa.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp