Gwamantin tarayya Nijeriya ta lashi takobin kawo karshen ambaliyar ruwa a kasar Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana hakan ta bakin mataimakin sa Sanata Kashim Shettima a yayin da ya yi saukar gaggawa a birnin Maiduguri inda ya kai ziyarar gani-da- ido kan ambaliyar da ta rutsa da dubban mutane a garin.
Shattima ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta sa kafar wando-daya da kalubalen ambaliyar ruwa a kasar ta hanyar amfani da taswirar da za ta kawo maslaha ta dindindin.
Read Also:
Shettima, wanda ke jawabin cikin kaduwa a lokacin da yake tantance irin barnar da ambaliyar ta yi a garin Maiduguri, ya jajanta wa wadanda ibtila’in ya rutsa da su, inda ya bayyana musu cewa, shugaba Tinubu na tare da al’ummar da abin ya shafa, kuma gwamnatin tarayya za ta samar da dukkan abinda ake bukata domin tabbatar da tsaro da tallafawa mutanen da lamarin ya shafa.
Shettima ya danganta ambaliyar da ballewar madatsar ruwa ta Alau wanda ya ta’azzara lamarin har ya zarce irin wanda aka taba samu a baya. Sai dai kuma ya jaddada aniyarsa ta samar da mafita mai dorewa.
haka kuma ya yi kira da a ci gaba da wayar da kan al’umma kan karuwar barazanar da sauyin yanayi ke haifarwa tare da jaddada aniyar gwamnati ta magance wadannan kalubalen gaba daya.
Shettima, ya kuma yaba wa gwamnati da al’ummar jihar Borno bisa namijin kokarin da suka nuna wajen daukar matakan da suka dace akan lokaci tare da kai dauki ga al’ummar da lamarin ya shafa a cikin gaugawa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 27 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 8 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com