Aƙalla ma’aikan jihar Kano 4,000 da gwamnatin tsohon gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ta tsawaita wa wa’adin aiki ne ake sa ran za su ritaya a ranar 1 ga Disamban 2024.
Gwamnatin jihar ta ce ta kammala bincike da tantace ma’aikatan, waɗanda aka yi wa ƙarin wa’adin aiki bayan sun kai shekara 35 suna aiki, ko kuma sun kai shekara 60 a duniya.
Ganduje ne ya assasa shirin tsawaita wa’adin aiki a jihar, inda ma’aikata za su iya cigaba da aiki har na tsawon shekara biyar bayan sun kai lokacin ritaya.
Bayan gwamna Abba Yusuf ya ɗare karagar mulki a ranar 29 ga Mayun 2023 ne ya soke wannan ƙudurin, sannan ya yi umarni a dawo da shekarun ritayar shekara 35 ana aiki ko kuma shekara 60 a rayuwa.
Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban Ma’aikatan jihar, Abdullahi Musa ya ce bayan an soke ƙudurin ne, aka kafa kwamiti domin kididdige adadin ma’aikatan.
“Bayan bincike ne kwamitinmu ya gano cewa kusan ma’aikata 4,000 suke cikin wannan tsarin, amma za su yi ritaya a 1 ga Disamban 2024. Wannan na nufin a ƙarshen watan Satumba za su miƙa takardar ajiye aiki,” inji shi kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sai dai Abdullahi Musa ya ƙara da cewa gwamnati ta shirye maye gurbin da za su bari bayan sun yi ritayar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 17 hours 48 minutes 19 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 29 minutes 44 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com