Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da mutum 67 ne suka kamu da cutar kyandar biri daga cikin mutum 1,031 da aka yi fargabar sun kamu da cutar a jihohi 23, ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa, NCDC ce ta bayyana hakan inda ta ce jihohin Akwa-Ibom da Enugu kowacce na da mutum takwas da suka kamu, sai Bayelsa da ke da shida, sai kuma Cross-River mai biyar, da kuma sauran mutum 40 ɗin da suka watsu a sauran jihohi 19.
Darakta Janar na NCDC, Jide Idris ya ce hukumar ta ƙara zage damtse domin yaƙi da yaɗuwar cutar.
“Muna aiki tare da hukumomin tashashin jiragen ruwa domin kiyaye yiwuwar shigo mana da nau’in Clade I na cutar,” inji Idris, inda ya ƙara da cewa suma hukumomin na tashashin jiragen ruwa suna tattaunawa da jihohin da suke bakin boda.
Ya kuma ce suna ƙara inganta ɗakunan gwaje-gwajensu a faɗin ƙasar domin tabbatar da cewa ba sai an yi ta yin jigila ba domin gwajin cutar.
Zuwa yanzu dai ƙasashe 13 ne suka fama da cutar kyandar biri a Afirka bayan ƙasar Guinea ta sanar da mutum na farko da ya kamu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 3 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 45 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com