Home General Harin ƙwanton ɓauna yayi sanadiyyar sojoji 3 da ‘yan sanda 7 a...

Harin ƙwanton ɓauna yayi sanadiyyar sojoji 3 da ‘yan sanda 7 a Zamfara

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar jami’anta 4 da na sojoji 3, a ƙoƙarinsu na daƙile harin da ƴan bindiga suka kai wani kamfanin gine-gine da ke kan babbar hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Mohammed Dalijan ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ƴan bindigar sun yi wa jami’an tsaron kwantan ɓauna ne a lokacin da suka yi yunkurin kai ɗauki wurin da ƴan bindigar suka kai hari.

Sai dai ƙwamishinan ƴan sandan ya tabbatar da cewar jami’an tsaron sun yi kokarin daƙile harin da ƴan bindiga suka kai kamfanin gine-ginen na Setraco.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Ƴandoto da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe na jihar Zamfara, da misalin ƙarfe 9 na safiyar jiya Alhamis.

wannan nan dai shi ne harin na biyu da ƴan bindigar suka kai kan babbar hanyar Funtua zuwa Gusau` cikin ƴan sa’oi, inda suka yi garkuwa da matafiya da dama da ke amfani da hanyar.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp