Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya rushe majalisar dokokin ƙasar da ƴan adawa ke da rinjaye a cikinta, tare da sanar da ranar 17 ga watan Nuwamba don gudanar da zaɓensu.
Faye wanda ya lashe zaɓen ƙasar da aka gudanar a watan Maris na wannan shekarar, tare da faraministansa Ousmane Sonko, sun yi wa ƴan ƙasar alkawarin kawo sauyi mai ma’ana.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
To sai dai gwamnatin su na fuskantar koma baya wajen aiwatar da manufofinta, sakamakon rashin rinjayen da su ke da shi a zauren majalisar.
A cewar kundin tsarin mulkin Senegal, Faye na da ikon rushe majalisar dokokin da ke da rinjayen ƴan adawa, tare da sanya ranar da za a gudanar da zaɓensu don samun rinjayen da suke buƙata, wanda hakan kuma zai basu damar aiwatar da kudurorinsu.
PRNigeria Hausa










