Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ci kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) tarar Naira Biliyan 1.69 bisa laifin tsauwala wa abokan hulɗarsu kuɗin wuta
Gidan talbijin na Channels ya rawaito cewar tarar ta ta’allaka ne a kan rashin bin umarnin da hukumar ta bayar a baya na iyakance kiyasin lissafin kuɗi ga masu amfani da wutar lantarki.
Hukuncin, wanda aka zayyana a cikin takarda mai suna ‘Order NERC/2024/114’, wani ɓangare ne na umarnin hukumar na watan Satumba na shekarar 2024.
Umurnin mai kwanan watan Agusta 30, ya samu sa hannun mataimakin shugaban NERC Musiliu Oseni da kwamishinan shari’a da lasisi da bin doka, Dafe Akpeneye.
Tarar ta fito ne ta shafin intanet na NERC kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Binciken da NERC ta yi kan tsarin biyan kudi na AEDC ya nuna cewa kamfanin tsalawa kwastomomi fiye da kima a tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na 2023.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 17 hours 50 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 32 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com