Home General Sojojin Nijeriya sun tarwatsa masarrafar Bom ta ISWAP a jihar Borno

Sojojin Nijeriya sun tarwatsa masarrafar Bom ta ISWAP a jihar Borno

Dakarun sojin Nijeriya sun sami nasarar tarwatsa masarrafar bom mallakin kungiyar tayar da kayar baya ta ISWAP a mashigar Abulam zuwa BUK dake karamar hukumar Damboa a jihar Borno dake Arewa maso gabashin kasar.

Wannan dai na daga cikin kokarin rundunar na kakkabe ayyukan ‘yan ta’adda a yankin tafkin Chadi dake fama matsalar rashin tsaro.

Zagazola makama ya ruwaito cewa dakarun na cigaba da samun nasarar ne tare da bankado ayyukan ‘yan ta’addan bisa hadin gwiwa da dakarun HUBRID da na JTF karkashin Operation Deset Sanity III hadin gwiwa da Operation Hadin Kai wannan yasa suke kara kutsawa maboyar ‘yan ta’addan.

Ayyukan dakarun sojojin dake karkashin kulawar rundunar sojojin saman Nijeriya ya sami gagarumar nasarar inda ya bankado maboyar ‘yan ta’addan dake yankunan Timbuktu da suka hadar da Talala, Gorgi duk dake kusa da dajin Sambisa.

A yayin sumamen sojoji da ‘yan bindigar sun yi musayar wuta inda suka hallaka da dama yayin da wasu kuma suka tsere da raunin harbin bindiga a jikin su, haka kuma a BUK sojojin sun bankado inda ‘yan ta’addan ke sarrafa Bom tare da kwato masu tarin yawa.

Daga nan sojojin sun isa zuwa maboyar kwamandan ‘yan ta’adda Abu Aisha dake Dusula, sai dai kafin su karasa tuni sun gudu don tserewa yin gaba da gaba da sojojin.

Zagazola ya ruwaito cewa sumamen sojojin ya sa sun tarwatsa maboyar kwamandojin mayakan na ISWAP da suka hadar da Hanzala Kaid, Abu Ibrahim, Baa Idrissa, Rawana, Mallam Abubakar da Abu Aisha wanda suka gudu ta yankunan Abba Gajiri da Bulabulin.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp