Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso ya nuna kwarin gwiwa cewa ƴan Nijeriya za su canja yanayin mulkin ‘kama-karya’ da APC ke yi a shekarar zabe ta 2027.
Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke karɓar mabiya jam’iyyar APC 977 na Ƙananan Hukumomin Dala da Kiru da su ka bar jam’iyyar zuwa NNPP a Kano a yau Alhamis a gidan sa da ke Miller Road.
Jagoran na NNPP ya kuma bayyana cewa an buɗe kofar tuba a Kwankwasiyya kuma zasu ci gaba da karɓar masu sauya sheƙa.
Read Also:
A cewarsa, gwamnatin APC ta gaza gurin cika alkawuran da ta daukar wa ƴan Nijeriya, inda ya yi kira ga ƴan ƙasa da su yi ƙoƙari su canja gwamnatin a 2027.
“Talauci, yunwa, rashin tsaro da rashin aikin yi sai ƙaruwa su ke. Magidanta ba sa samu su ciyar da iyalan su.
“Wannan lokaci ne da ƴan Arewa da ma Nijeriya baki daya za su tashi tsaye su kawo canji da kan su.
“Su na ganin ba za a iya canja su ba saboda su na da tsaro da hukumar zabe, to idan guguwar canjin ta bisa su da kan su za su yi gudun famfalaƙi,” in ji Kwankwaso
PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 11 hours 51 minutes 7 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 32 minutes 32 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com