Home General Fubara ya gana da sabbin zababbun shuwagabannin kananan hukumomin Ribas

Fubara ya gana da sabbin zababbun shuwagabannin kananan hukumomin Ribas

Gwamnan Jihar Ribas Similary Fubara Ya Bukaci Sabbin Zababbun Shugabannin Kananan Hukumomi 23 da aka zaba a Jihar da su kasance Masu Sanya kishin Al’umma a gabansu

A Wani kwarya kawaryar Bikin da ya gudana a Dakin taro na gidan Gwamnatin Jihar Ribas, Gwamnan yace Zaben da akayi na Kananan Hukumomi a Jihar ya Bude wata Sabuwar Sabon Shafi na Sabuwar Jihar Ribas

Ya Kara Da Cewa Yanzu Jihar Ribas ta kasance Jiha Mai Yanci da Kuma Cin gashin kanta Wadda Kuma Zata Cigaba da zama da kafafuwanta.

Bayanin Gwamnan Jihar ta Ribas dai na zama Wani sako ga Tsohon Gwamnan Jihar ta Ribas Nyesom wike Dake zama Tsohon Mai Gidan Gwamnan na Yanzu Wanda Kuma Suka raba gari tin Kafin tafiya Tayi nisa.

Gwamnan yana Cewa Mulkin mallaka da Kuma San zuciya ya zama tarihi a Jihar Ribas Kuma zamu Cigaba da Samar da ayyukan raya Kasa tare da Hadin guiwar Sabbin Zababbun Shugabannin Kananan Hukumomi 23 da aka zaba a Jihar ta Ribas

Zaben Wanda ya kasance Mai cike da Kalubale musamman ta Fuskar Tsaro Kasancewar jami’an Tsaro na Yan Sanda sun janye jiki daga bayar da Tsaro a Zaben da ya Gabata.

Sai dai duk da haka Gwamnan ya Tabbatar da karfin ikonsa na Tabbatar da Gudanar da Zaben da Hukumar Zaben Jihar ta shirya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp