Home General Ƴan ta’addar da suka tsere daga Zamfara na yi wa Kano barazana

Ƴan ta’addar da suka tsere daga Zamfara na yi wa Kano barazana

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa-ido sosai a birnin Kano, bayan da wani rahoton da hukumomin tara bayan sirri suka gano cewa yanzu ɗimbin ƴan bindiga sun tsere daga Zamfara inda suke fakewa a cikin birnin wanda shi ne mafi girma a arewacin kasar.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ne ya sanar da hakan, bayan da ya samo kwafin wasikar da hukumomin tara bayanan sirri daga Zamfara suka tura wa takwarorinsu da ke Kano.

A cewar AFP, tun a ranar Litinin da ta gabata ne aka gabatar wa gwamnan jihar Kano da wannan rahoto, da ke cewa mafi yawan ƴan bindigar tuni suka mallaki gidaje a cikin birnin Kano, yayin da wasu ke fakewa a unguwannin Rijiyar Zaki, Tudun Yola, Ja’en, Ɗorayi Babba, Rijiyar Lemo da kuma Ƴan Awaki.

Bisa ga dukan alamu, rahoton ya ce mafi yawan ƴan bindigar sun nemi mafaka a birnin Kano ne saboda tsanantar hare-hare da jami’an tsaro ke kai musu a cikin ƴan kwanakin nan, yayin da wasu suka mallaki gidajen tsawon shekaru a birnin a daidai lokacin da suke taimaka wa ƴan bindigar da ke gudanar da ayyukan tsagarenci a jihohin Zamfara, Katsina da kuma Kaduna.

Wasu majiyoyi biyu na tsaro, sun tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran AFP da cewa rahoton ya shiga hannuwansu, yayin da wata majiyar ke cewa yanzu tana aiki tukuru domin zaƙulo su a cikin gaggawa.

To sai dai majiyar na cewa yanzu haka jami’an tsaro na aiki ne a asirce domin ka da jama’a su shiga hali na firgita.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp