Home Labarai Kotu ta hana PDP tsige Damagun a matsayin shugaban riƙo

Kotu ta hana PDP tsige Damagun a matsayin shugaban riƙo

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da kwamitin amintattu BOT da majalisar ƙolinta daga cire Umar Damagun a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar.

Mai shari’a Peter Lifu ne ya bayar da umarnin a hukuncin da ya yanke, inda ya ce Damagun ne zai cigaba da zama shugaban jam’iyyar na riƙo har zuwa ranar da za a gudanar da babban taron jam’iyyar a watan Disamban 2025.

Alƙalin ya ce bisa la’akari da sashe na 42 da 47 da 67 na jam’iyyar, a babban taron jam’iyyar ne kawai za a zaɓan wani sabon shugaba, inda ya ce dole duk wani ɗan jam’iyyar ya yi biyayya ga kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Mai shari’a Lifu ya ƙara da cewa yanzu zangon shugabancin PDP na Arewa ne, inda ya ƙara da cewa tunda an zaɓi Damagun ne domin ƙarasa zangon mulkin Iyorchia Ayu wanda shi ma ɗan yankin ne, dole ya ƙarasa zangon.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp