Sanata Ndume ya bukaci Tinubu ya tausayawa ‘yan Nijeriya

Ɗan majalisar dattijan Najeriya mai wakiltar Borno ta kudu, Sanata Ali Ndume ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya rage farashin man fetur, inda ya ce ƴan Najeriya na cikin wahala.

Ndume ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja, inda ya kuma ce ci gaba da ƙara farashin man fetur da abinci da kuma kayan amfani na yau da kullum na ƙara jefa ƴan Najeriya cikin kunci da wahala, musamman ma talakawa.

Tsohon mai tsawatarwa na majalisar ya ce wasu ɓata-gari cikin gwamnati na ƙoƙarin haddasa fitina tsakanin mutane da gwamnatin Tinubu ta hanyar ɓullo da tsare-tsare masu tsauri da kuma mara kyau maimakon shawo kan matsalar hauhawar farashi da kuma tashin kuɗin dala da ke ci gaba da kassara ƴan ƙasar.

“Wasu ne kawai ke son ɓata Tinubu a idon jama’a ta hanyar ɓullo da waɗannan tsare-tsare daga karshe kuma laifi ya koma kan shugaban.

“Ina kira ga shugaban ƙasa da ya daina kula waɗannan mutane da ke son kawo cikas ga gwamnatinsa.Halin kunci da mutanen ke sa ƴan Najeriya ba zai misaltu ba,” in ji Ndume.

Ya ce mutane na cikin matsanancin wahala musamman ma jihar sa ta Borno.

“Mutane na cikin matsi, akwai yunwa, ɓacin-rai da kuma fushi cikin al’umma,” in ji Sanatan.

Ya ce ya san shugaba Tinubu yana da manufa mai kyau ga ƴan Najeriya, sai dai wasu masu ba shi shawara ne ke son kassara ƴan ƙasar ta hanyar ba shi shawara mara amfani.

Sanata Ndume ya buƙaci shugaban ƙasar da ya duba batutuwan da zarar ya koma daga hutun da ya tafi da nufin shawo kan su.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 15 hours 9 minutes 9 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 50 minutes 34 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com