Ministan lafiya a ƙasar Zimbabwe ya sanar da ɓullar cutar ƙyandar biri karon farko a ƙasar.
Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa waɗanda aka samu da cutar sun haɗa da wani yaro mai shekara 11, da wni matashi mai shekara 24, waɗanda suka yi tafiya daga Afirka ta Kudu da Tanzania a cikin watannin Agusta da Satumba.
Sanarwar da ma’aikatar lafiyar ƙasar ta fitar ta ce: ”Yanzu haka an keɓe dukkan mutanen biyu kuma suna samun kula yadda ya kamata”
Sai dai ma’aikatar lafiyar ta ce ”abubuwa sun lafa” domin haka suke kira ga jama’ar gari ”kada su razana.”
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana dokar ta-ɓaci kan yaƙi da ƙyandar biri ne bayan cutar ta yaɗu daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo zuwa ƙasashe masu maƙotaka da ita.
Ita ma cibiyar yaƙi da yaɗuwar cutuka ta Afirka ta ayyana dokar ta-ɓaci a kan cutar, wadda ta ce tana barazana ga al’ummar nahiyar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 21 hours 10 minutes 11 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 22 hours 51 minutes 36 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com