Jam’iyya NNPP ta dakatar da sakataren gwamantin jihar Kano Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan sufuri na jihar Muhammad Diggol daga Jam’iyyar.
shugaban Jam’iyyar na jihar Kano Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya tabbatar da hakan ga wakilin PRNigeria a yau litinin.
Read Also:
tun da fari dai wani sakon murya ya karade kafafen sadarwa dake bayyana dakadar da sakataren gwamnatin da kwamishinan bisa wasu dalilai na rikicin cikin gida.
ya ce an dakatar da su ne bisa zargin kin yin biyayya da kuma aikata wasu abubuwa da suka saba dokar jam’iyyar da hada hargitsi a jam’iyyar.
“Muna sanar mu ku a yau mun dakadar da Sakataren gwamnatin jihar Kano Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan Sufuri, Muhammad Diggol bisa saba doka da kuma rashin yin biyayya ga Jam’iyyar”.
PRNigeria Hausa