Home Labarai Wani babban kwamandan RSF ya miƙa wuya ga sojojin Sudan

Wani babban kwamandan RSF ya miƙa wuya ga sojojin Sudan

Rundunar sojin Sudan ta ce ɗaya daga cikin kwamandan mayakan rundunar RSF Abuagla Keikal, ya miƙa wuya tare da wasu dakarunsa, wanda shi ne na farko da aka sami wani babban jami’inta da yayi, tun bayan da ɓangarorin suka faro rikici a tsakiyar watan Afrelun shekarar da ta gabata.

Rundunar sojojin Sudan wacce a ƴan kwanakin nan ta bayar da rahotan fara samun nasarar kwato wasu yankuna na babban birnin ƙasar Khartoum, ta ce Keikal ya ɗauki matakin ne sakamakon yadda rundunar RSF ta sauka daga kan tsarin da aka samar da ita.

Wasu daga cikin masu goyon bayan sojojin Sudan, sunta saka hotunan Keikal da ke jagorantar rundunar RSF a kudu maso gabashin jihar El Gezira, a kafofin sada zumunta, bayan sanar da matakin da ya ɗauka.

Kawo yanzu dai rundunar RSF da ta kwace iko da sassan ƙasar da dama da kuma shi kansa Keikal, basu ce komai game da lamarin ba.

Rikicin na Sudan ya sanya sama da mutane miliyan 10 barin muhallansu tare da jefa wasu da dama cikin matsananciyar yunwa, lamarin da ya sanya Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yakin da ake gwabzawa a Sudan din tsakanin sojoji da dakarun RSF,  ya haifar da ɗaya daga cikin matsalolin ayyukan jin kai mafi muni a duniya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp