Gwamnatin Nijeriya ta hana fitar da gas din girki kasashen waje

Gwamnatin Najeriya ta hana fitar da gas ɗin girki zuwa ƙasashen waje, daga ranar 1 ga watan Nuwamba mai kamawa, a wani mataki da ta ce ta ɗauka domin hana hauhawara farashin gas ɗin.

Ƙaramin ministan albarkatun mai mai kula da harkokin gas, Ekperikpe Ekpo, ne ya bayyana haka, a cikin irin matakan da ya ce gwamnati ta ɗauka domin tabbatar da saukinsa.

Ministan ya nuna damuwarsa kan yadda farashin gas ɗin ke ta hauhawa a baya-bayan nan daga tsakanin naira 1,100 da 1,250 zuwa naira 1,500 a kan kilo ɗaya.

A kan hakan ministan ya yi taro da masu ruwa da tsaki a kan gas ɗin a Abuja ranar Talata kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, domin lalubo hanyoyin magance matsalar hauhawara farashin, wadda ke damun ‘yan ƙasar.

A nan ne ministan ya sanar da cewa daga cikin muhimman matakan da aka ɗauka sun haɗa da umartar kamfanin mai na ƙasar NNPCL da masu samar da gas ɗin na cikin ƙasa da su daina fitar da gas ɗin da aka samar a ƙasar zuwa waje.

Ekpo ya jaddada buƙatar ganin an samar da wani tartibin tsari na tsayar da farashin gas ɗin wanda zai dace da cikin gida.

A wata sanarwa da kakakin ministan, Louis Ibah, ya fitar ya ce an bai wa hukumomin da ke aikin hakowa da sayar da albarkatun mai na ƙasar da su fitar da wani tartibin tsarin farashin gas ɗin na cikin gida nan da kawana 90.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 22 minutes 27 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 3 minutes 52 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com