Gwamnatin jihar Kano ta bukaci al’ummar jihar da su tabbatar an yiwa yaran su allurar rigakafin cutar inna wato Polio, domin gujewa yaduwar cutar a cikin al’umma.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai, a wani bangari na bikin ranar yaki da cutar ta Shan inna a jihar Kano.
Dr. Abubakar labaran ya ce wannan rana na da matukar muhimmancin wajen tunatar da al’ummar yadda wannan cuta ke kassara dan adam da zarar ta shiga jikin sa.
“Mun hadu yau 24 ga watan 10 na shekarar 2024 domin mu tunatar da kan mu, muhimmancin wannan rana da aka ware musamman saboda cutar shan inna”
“ita wannan cuta, cuta ce wadda kwayar cuta da ake kira “Poliovirus” take janyowa, wadda idan ta shiga jikin dan Adam take janyo nakasu, take bin laka ta jikin dan Adam ta kassarashi, wani ta janyo masa rashin kafa wani rashin hannun, wani ma hannun da kafafuwan su shanye”.
Ya kara da cewa wajibi ne akan ma’aikatan lafiya a jihar kano su tabbatar da an kawar da cutar, daga cikin al’umma domin kaucewa hadarin da take dauke da shi.
Read Also:
“Wannan aiki abu ne mai yiwuwa, kuma za’a iya yin sa, domin ya zama dole akan mu, mu ma’aikatan gwamnati, ma’aikatan lafiya ‘yan jarida da kuma iyaye wanda Allah ya dora musu Alhakin tabbatar da cewa sun samawa ‘ya’yansu makoma mai kyau”
Ya kuma ce tuni cutar ta bar jihar kano, bisa kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da an inganta hanyoyin yaki da cutar, musamman ta hanyar hadaka da kungiyoyin duniya, irin sun Melinda Gate, wanda hakan yayi tasirin gaske wajen magance cutar a jihar.
Sai dai kwamishinan yace a ‘yan tsakanin an sami alamun bullar cutar a jihar Kano, wanda kuma suke zargin wasu baki ne suka shigo da ita jihar; Wanda yace kananan yara na jihar na cikin hadarin kamuwa da cutar muddin ba’a dauki matakin da ya dace ba.
“Wannan dalilin ne yasa muka ga dole mu sanar da al’umma, kuma mu yi kira garesu cewa su tabbatardukkanin yara musamman wadanda ke kasa da shekaru 5 a duniya da zarar jami’an dake allurar sun isa inda yaran suke”.
Daga bisani ya tabbatar da cewa yaran da aka samu sun kamu da wannan cuta, basu haura shekaru biyar zuwa bakwai a duniya ba, wanda hakan ke da nasaba da rashin mayar da hankali a yin allurer ta rigakafin cutar shan inna.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 41 minutes 44 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 23 minutes 9 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com