Majalisar dattawan Najeriya ta ce tana son yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyara fuska, ta yadda za a samar da dokar hukuncin ɗauri ga iyayen da suka ƙi sanya ‘ya’yansu a makaranta.
Shugaban kwamitin ilimi na majalisar, Sanata Lawan Adamu Usman ya ce majalisar na duba yiwawar sanya hukunci ɗaurin wata shida ga duk iyayen da suka kasa sanya ‘ya’yansa a makaranta.
Yayin da yake zantawa da manema labarai, bayan gabatar da rahoton kwamitinsa a gaban majalisar a ranar Laraba, Sanata Lawan ya ce “muna son a yi dokar ɗaurin wata shida ga iyayen da suka ƙi sanya ‘ya’yansu a makaranta. Shi ma ilimi masu iya magana na cewa shi ne gishirin rayuwa, kuma shi ne maganin duka matsalolin da ke faruwa a ƙasar nan,” in ji sanatan.
Tun da farko shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya ce akwai yara fiye da miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, waɗanda ya ce idan ba a ɗauki matakin kula da su ba, za su iya zama ɓata-gari idan suka girma.
Shi ma Mataimakain Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya ce matsalar rashin zuwan yara makaranta, babbar damuwa ce ga ƙasar, wanda ya ce ta fi ƙamari musamman a yankin arewacin ƙasar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 32 minutes 46 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 14 minutes 11 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com