Shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya ba da tabbacin a jiya Juma’a cewa, za a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki na ranar 17 ga watan Nuwamba, cikin ‘yanci da gaskiya, yana mai kira ga ‘yan siyasa da su kiyaye daga duk wani lamari da kan iya haifar da tashin hankali ko rudani.
Shugaban na Senegal ya na mai cewa “yayin da yakin neman zaben ‘yan majalisar dokoki ke gabatowa, ina gargadin dukkan ‘yan kasar Senegal, musamman ma ‘yan siyasa na ko wane bangare, da su guji wuce gona da iri a cikin maganganunsu da ayyukansu.”
Read Also:
Faye ya yi amfani da wannan dama tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki da su kawo ta su goyon baya na ganin an cimma nasara a wannan zabe da sunan ceto kasar ta Senegal a karshe da kuma tabbatar da cewa “zaben zai kasance cikin ‘yanci, dimokiradiyya da gaskiya”.
A ranar 17 ga watan Nuwamba ne ‘yan kasar Senegal za su zabi sabuwar majalisar dokoki, watanni takwas bayan zaben shugaban kasar da Diomaye Faye ya yi nasara a zaben shugaban kasa da aka yi a zagayen farko da kashi 54% na kuri’un da aka kada. Za a fara yakin neman zaben a yau Asabar da dare.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 25 minutes 32 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 6 minutes 57 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com