Mutum 10 sun mutu, yayin da bakwai suka jikkata bayan rushewar gini a Ibadan

Aƙalla mutum 10 ne suka mutu yayainwa su bakwai suka jikkata bayan faɗuwar gini a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Cikin wata sanarwa da hukumar kashe gobara ta jihar ta fitar, ta ce lamarin ya faru da tsakar daren da ya gabata a unguwar Jegeda Oluloyo da ke binrin na Ibadan, kamar yadda Jaridar unch ya ruwaito.

Sanarwar ta ƙara da cewa yayin da aka zaƙulo gawarwarkin mutum 10 daga cikin ɓaraguzan ginin, an kuma ceto wasu mutum bakwai da raunuka, sannan an ci gaba da aikin ceton domin nemo ƙarin mutane.

Faɗuwar gine-gine dai wani lamari ne da ke neman zaman ruwan dare a Najeriya, inda da dama takan zo da asarar rayuka masu yawa.

Mahukuntar ƙasar na ɗora alhakin matsalar kan rashin bin ingantaccen tsari da ƙa’ida a lokacin yin gine-ginen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com