Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya nuna gamsuwa da yadda shirin rigakafin shan-inna yake tafiya a ƙananan hukumomin Ajingi, Gaya da Wudil.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran hukumar lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi, wadda tace Kwamishinan ya nuna gamsuwar ne a ranar Lahadin da ta gabata jim kaɗan bayan kammala duba aikin a wasu sassa na ƙananan hukumomin.
Ya ce ya ji daɗi sosai da yadda ya ga jama’a sun karɓi shirin hannu bibiyu, wanda shi ne jigon samun nasarar shirin a yankin, yana mai yaba wa ma’aikatan lafiya na ƙananan hukumomin wajen tabbatar da yi wa dukkanin yaran da suka cancanta rigakafin.
Kwamishinan ya jinjina wa shugabancin ƙananan hukumomin saboda kyakkyawan aikin da suka yi na bin tsare-tsare da aiki tare kamar yadda aka tsara tun daga matakin jiha, da kuma yadda suke halartar tarukan nazarin yadda aikin ya gudana a kowace rana.
Ya ce, “Abin farin ciki ne ganin yadda shugaban ƙaramar hukumar Gaya yake zuwa ko ina a yankin domin tabbatar da an yi wa yaran da suka cancanta rigakafin ba tare da tsallake yaro ko daya ba. Ƙari kan haka, shugaban ƙaramar hukumar yakan bayar da tallafin magunguna da kayayyakin aiki a asibitoci don inganta harkokin lafiya a yankin.
Read Also:
“Bugu da ƙari, an ga mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Wudil yana kai kawo a lungu da saƙo na yankin domin tabbatar da shirin ya cimma nasara a yankin.
Dakta Labaran, wanda Daraktan Daƙile Cututtuka Masu Yaduwa na Ma’aikatar Lafiya, Dakta Ibrahim Aliyu Gano ya wakilta, ya yaba wa jajircewar hakiman yankunan game da rawar da suke takawa don samun nasarar shirin a matsayinsu na iyayen ƙasa, da kuma yadda suke halartar tarukan duba yadda aikin ya gudana a kowace rana, inda a wasu lokutan suke tura wakilai idan ba za su samu damar zuwa ba.
Ya buƙaci iyaye da su ci gaba da kai yaransu da suka cancanta cibiyoyin yin rigakafi da aka ware ko kuma su bar ma’aikatan da ke bi gida-gida suna yi wa yaran rigakafin domin a daƙile ɓurɓushin cutar shan-inna da aka fara samu a wasu sassa na jihar nan, don haka akwai buƙatar haɗa hannu wajen tukarar matsalar.
Daga nan sai kwamishinan ya buƙaci jami’ai masu wayar da kan mutane kan kiwon lafiya a yankunan da su ƙara ƙaimi wajen ilimantar da al’umma su fahimci baƙatar da ake da ita ta su bai wa ma’aikata masu bi gida-gida cikakken haɗin kai domin kuɓutar da yaransu daga wannan cuta mai illa.
Dakta Labaran ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Abba Kabir Yusuf na yadda ya mayar da fannin lafiya ɗaya daga cikin manyan ƙudurorin da gwamnatinsa ta bai wa fifiko wanda tuni kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 8 hours 54 minutes 56 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 10 hours 36 minutes 21 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com