Baban layin lantarki na Najeriya, ya sake faɗuwa, lamarin da ya sake jefa wasu sassan ƙasar cikin rashin wutar lantarki.
Faɗuwa – wadda ta auku da misain karfe 11:28 na safiyar yau Alhamis – ita ce ta biyu cikin mako guda, sannan ta 10 a 2024.
Read Also:
Bincike da aka yi kan shafin ‘Independent System Operator’, wanda sashe ne na TCN ne mai kula da fannin rarraba wutar, ya nuna cewa babu wuta a duka tasoshin samar da wuta daga babban layin.
Kawo yanzu dai kamfanin rarraba wutar na TCN bai yi bayanin dalilin faɗuwar ta baya-bayan nan ba.
Faɗuwar babban layin na lantarki na neman zama wata matsala ta yau da kullum a Najeriya, wani abu da ‘yan ƙasar da dama ke ɗora alhakinsa kan gwamnatin ƙasar.