Home General Gwamnan Kano ya haramta kalmar “Abba Tsaya Da Kafarka”

Gwamnan Kano ya haramta kalmar “Abba Tsaya Da Kafarka”

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce cin fuska ne fada masa kalmar “Abba Tsaya Da Kafarka” kamar yanda wasu suke Faɗa.

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a daren Laraba a fadar Gwamnatin Jihar Kano.

Abba ya ce shekaru 40 na kwashe tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Kuma Muna Tare Dashi har yanzu.

“Ina mamakin yadda wasu suke cewa na Tsaya da Kafata Kuma wanna Cin Fuska ne gare ni, domin kuwa Kwankwaso Mai gidana ne Muna zaune Lafiya dashi Dan Haka Babu Wata Baraka a tsakanin mu”

“Daga Yau Laraba 6-11-2024 Duk Wani jami’in Gwamnati ko abokan Arziki ko masoya na haramta  masa Kara Cewa na Tsaya da Kafata.

” Kwankwaso shine Jagoran mu Kuma shine Shugaban mu, Amma Saboda son zuciyar Wasu Suke Kokarin Kawo Mana rikici a Jam’iyyar NNPP.”

“Dan Haka nake Muku rantsuwa da Cewa wallahi bani da masaniya akan abinda Wasu Ke Cewa wai Akwai rigima tsakanina da Kwankwaso.”

Abba ya ce yayi niyyar maka jaridar da ta wallafa cewa yaki daukar kiran Kwankwaso a kotu amma wasu dalilai ne suka hana.

“Nayi niyyar zuwa Kotu akan Cewa wai Kwankwaso ya kirani sau 33 ban dauka ba, to amma na hakura Saboda Yadda nake girmama Yan Jarida”

PRNigeria hausa
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp