Home General Gwamnatin Najeriya za ta fara yi wa mata tiyatar haihuwa kyauta

Gwamnatin Najeriya za ta fara yi wa mata tiyatar haihuwa kyauta

Ma’aikatar lafiya a Najeriya ta ƙaddamar da wani shiri na yi wa mata masu ciki tiyata kyauta a faɗin ƙasar.

Shirin da aka yi wa take da Maternal Motality Reduction Innovation Initiative (Mamii), an ƙaddamar da shi yayin wani taron bita na shekara-shekara a Abuja.

Ministan Lafiya Muhammad Ali Pate ya bayyana shirin da zimmar rage mutuwar mata yayin haihuwa a faɗin Najeriya.

“Babbar manufar wannan shiri ita ce yi wwa mata marasa ƙarfi tiyatar haihuwa kyauta, amma waɗanda suka cika ƙa’ida a asibitocin gwamnati da na kuɗi,” a cewar ministan.

“Ta hanyar cire matsalolin kuɗi, muna ganin babu wata mace da ya kamata a bari ba tare da an kula da ita ba ko da ba ta da kuɗi.”

Ya ƙara da cewa mutuwa yayin haihuwa na ci gaba da zama barazana, inda ƙananan hukumomi 172 ke haifar da kashi 50 cikin 100 na dukkan mace-macen da ake samu wajen haihuwa a faɗin ƙasar.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp