Kungiyar Likitoci na jihar Kano sun janye yajin aikin da suka fara a daren jiya, bayan Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ya sami nasarar sasanta rikicin dake faruwa, tsakanin kungiyar da kuma Kwamishiniyar Ma’aikatar Jin-kai ta jihar.
Shugaban Kungiyar Likitoci na jihar Kano Dakta Abdurrahman ne ya tabbatar da hakan, a yayin zantawar sa da manema Labaran a fadar Gwamnatin Kano.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar da Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aiko wa jaridar PRNigeria ta kara da cewa, yanzu haka Likitocin sun koma bakin aiki domin ci-gaba da bawa marasa lafiya cikakkiyar kulawar da suka saba.
Dakta Abdurrahman ya ce sun janye yajin aikin ne bayan wani zama na musamman da Gwamnan Kano, akan sabanin da aka samu a tsakanin Mambar tasu da kuma ita waccan Kwamishiniya.
Ya kuma yaba wa Gwamnan a bisa gaggawar daukar matakin da ya kamata akan lamarin, harma yayi kira ga al’ummar jihar da su dinga bin dukkan hanyoyin da suka dace wajen shigar da korafin su akan jami’an lafiya domin a sami damar yin adalci ta hanyar bincika wa dama daukar matakin da ya kamata.











