Abba ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 ga majalisar Jihar Kano

Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin Naira biliyan 549 na kasafin kudi na shekarar 2025 ga majalisar dokokin jihar domin amincewa da shi.

Kasafin da aka yi wa lakabi “Kasafin Fata”, Gwamna Yusuf ya ce an samar da shi ne domin inganta rayuwar al’ummar jihar.

Gwamnan ya ce kasafin ya kunshi Naira biliyan 312 na manyan ayyuka da kuma Naira biliyan 236 na kudaden da ayyukan yau da kullum.

Gwamnan ya bayyana cewa mafi yawan kudaden dake kunshe cikin kasafin kudin kimanin naira biliyan 461, za a kashe su ne a bangaren walwalar jama’a da bunkasa tattalin arziki jihar.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com