Shugaban iyalan gidan su tsohon babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftana Janar Taoreed Lagbaja, Pa Tajudeen Lagbaja, ya ce ya yi nadamar saya wa marigayin takardar neman shiga makarantar horad da ƙananan hafsoshin sojan Najeriya, (NDA).
Pa Tajudeen, wanda ƙani ne ga mahaifin marigayin ya ce da ya san hakan zai kai ga rasuwar Janar Lagbaja da tun da farko bai sai masa fom ɗin ba.
Haka kuma wasu dangi ko iyalan marigayin sun yi zargin cewa wataƙila an kashe Laftana Janar Lagbaja ne ta wata muguwar hanya saboda rikicin wani fili a garinsu.
Read Also:
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jaridar The Nation, ta bayar da labarin cewa a 2023 wani rikici ya tashi a garin Ilobu, hedikwatar ƙaramar hukumar Irepodun da ke jihar Osun, a lokacin da wakilan rundunar sojin ƙasa ta Najeriya suka shirya gina asibiti a garin.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa marigayi Lagbaja a matsayin babban hafsan sojin ƙasar a watan Yuni na 2023,inda ya maye gurbin Laftanar Janar Faruk Yahaya, wanda tsahon shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya naɗa a 2021.
Rahotanni sun ce tun bayan ba shi muƙamin, ya riƙa fama da rashin lafiyar da take kawo masa tsaiko wajen gudanar da aikinsa, lamarin da ke sanyawa yana yawan fita ƙasashen ƙetare neman magani.
Gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwa cewa babban hafsan sojin na ƙasa ya rasu ranar 5 ga watan nan na Nuwamba, 2024, yana da shekara 56 a wani asibiti a Lagos, bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 5 minutes 31 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 46 minutes 56 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com