Babban Sufeton ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ya haramta wa ƙungiyar tsaro ta jihohin kudu maso yamma da ake wa lakabi da Amotekun da ‘yansintiri na Vigilante da sauran ire-irensu shiga harkokin zaɓen gwamnan jihar Ondo.
Read Also:
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan na ƙasa Auyiwa Adejobi ya fitar a yau Lahadi, ya ce Babban Sufeton ya bayar da umarnin tura jami’an ‘yansanda daga ɓangarori daban-daban na rundunar domin aikin zaɓen.
Aƙalla jam’iyyu 17 ne aka bayar da rahoton cewa za su shiga zaɓen wanda za a yi ranar Asabar mai zuwa, 16 ga watan Nuwamba, 2024.
Sanarwar ta ce ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro na tarayya ne za su aikin tabbatar da tsaro a lokacin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 20 hours 42 minutes 56 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 22 hours 24 minutes 21 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com