Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu ya ciyo bashin dala biliyan 2.2.
Majalisar dattijai ta amince da bukatar ciyo bashin ne bayan da ta yi nazari kan rahoton Aliyu Wamakko, shugaban kwamitin kula da basussukan cikin gida da na kasashen waje.
Read Also:
Kudaden da Tinubu zai ciyo bashin a kudin Naira ya kai kwatankwacin Naira Tiriliyan 1.7 , za dai a yi amfani da Kudaden ne domin cike gibin Naira Tiriliyan 9.1 a kasafin kudin 2024.
A ranar talata ne dai Shugaba Tinubu ya bukaci majalisar dattawan da ta amince masa ya ciyo wannan bashin.
Majalisar zartaswa ta Nigeriya (FEC) ce ta fara amincewa a da shirin karɓo bashin na dala biliyan 2.2 don “karfafa kudaden kasar da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar”.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 minutes 7 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 2 hours 3 minutes 32 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com