Matakan bunƙasa tattalin arzikin ka na matuƙar illa ga talakawan Arewa – ACF

Ƙungiyar kare martabar ƴan Arewacin Najeriya ta ACF, ta buƙaci shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta sake fasalin matakan da yake ɗauka domin bunkasa tattalin arzikin ƙasar, saboda abinda suka kira matuƙar illar da yake yiwa talakawan da ke yankin.

Bayan wani taro da ta gudanar, wanda ya yi nazari a kan irin manufofi da matakan da gwamnatin ke ɗauka, ƙungiyar ta ce rayuwar talakawan Najeriya na kara tabarbarewa musamman mazauna yankin arewacin ƙasar da ke fuskantar ƙalubale daban daban.

Sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya rabawa manema labarai, ta ce mazauna yankin arewacin ƙasar na fama da tsananin rashin abinci da tsaro da ƙarancin samun damar ilimi da koyan sana’o’i da kuma harkokin kasuwancin da za su dogara da kansu.

Muhammad-Baba ya ce rayuwar akasarin mutanen arewacin ƙasar ya dogara ne ga ƙananan sana’oi, amma yanayin da ake ciki ya jefa da dama daga cikin su cikin halin ƙaƙanikayi da kuma rashin madogara, sakamakon manufofin tattalin arzikin da wannan gwamnatin ke ɗauka a matakin tarayya, ba tare da la’akari da irin uƙubar da yake jefa jama’a ba.

Ƙungiyar ta ce duk da yake ɗaukar irin waɗannan matakai na da matukar tasiri, amma kuma bai da ce ya yi illa ga mutanen da ake cewa ana yi domin su ba, saboda yanayin da ake ciki na iya hallaka wasu daga cikin su ta hanyar da ba za su iya cin moriyar gajiyar da za’a samu ba.

Muhammad-Baba ya ce sun buƙaci shugaban ƙasar da ya sake nazarin takunsa ta hanyar da zai dinga la’akari da rayuwar jama’a, tare da kuma sauraron ƙorafin jama’a domin gyara ga matakan da suke ɗauka waɗanda ke yiwa ƴan ƙasa illa.

ACF ta buƙaci ɗaukar matakan gaggawa ta hanyar aiwatar da manufofin kar-ta-kwana da kuma na dogon zango ta hanyar da za’a samarwa jama’a abinci, ciki hara da shigo da shi daga ƙasashen ƙetare, domin ragewa jama’a raɗaɗin halin da suke ciki.

Ƙungiyar wadda ta ce ta fahimci ƴan arewa ne kawai za su kare martabar yankin, ta buƙaci samun daidaito wajen raba mukamai da kuma gaggauta samo maslaha dangane da matsalar samar da wutar lantarki da talaucin da ya addabi jama’a da rashin ayyukan yi da kuma koma bayan da yankin ke fuskanta.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 56 minutes 7 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 2 hours 37 minutes 32 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com