Majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin dokar da ke neman mayar da wa’adin shugabancin Najeriya ya koma shekaru shida, amma falle daya.
An yi watsi da kudirin dokar, wanda ake shirin yiwa karatu na biyu a yayin zaman taron na ranar Alhamis.
Kudirin dokar dai da ya wuce zai sauya tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Nigeriya, na samar da wa’adin mulki na shekaru shida ga shugaban kasa da gwamnonin jihohi.
Read Also:
Hon. Ikenga Ugochinyere ne ya gabatar da kudirin , Wanda ya bukaci wa’adin mulkin Shugaban kasa da gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi ya koma falle daya amma ya kai shekaru shida .
Kudirin ya kuma nemi a ba da damar gudanar da dukkan zabukan shugaban kasa, gwamna da yan majalisu duk a rana daya.
A lokacin da aka kada kuri’a a kan kudirin dokar da aka shirya yi wa karatu na biyu, yawancin ‘yan majalisar sun kada kuri’ar kin amincewa da shi.
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayar da shawarar a gyara kundin tsarin mulkin kasar na 1999 da dokar zabe ta 2022, saboda a bada dama wa’adin shugaban kasa ya koma na tsawon shekaru shida, sannan a rika baiwa kowacce shiyya dama.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1489 days 20 hours 37 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1471 days 22 hours 18 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com