Home General Matakan bunƙasa tattalin arzikin ka na matuƙar illa ga talakawan Arewa –...

Matakan bunƙasa tattalin arzikin ka na matuƙar illa ga talakawan Arewa – ACF

Ƙungiyar kare martabar ƴan Arewacin Najeriya ta ACF, ta buƙaci shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta sake fasalin matakan da yake ɗauka domin bunkasa tattalin arzikin ƙasar, saboda abinda suka kira matuƙar illar da yake yiwa talakawan da ke yankin.

Bayan wani taro da ta gudanar, wanda ya yi nazari a kan irin manufofi da matakan da gwamnatin ke ɗauka, ƙungiyar ta ce rayuwar talakawan Najeriya na kara tabarbarewa musamman mazauna yankin arewacin ƙasar da ke fuskantar ƙalubale daban daban.

Sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya rabawa manema labarai, ta ce mazauna yankin arewacin ƙasar na fama da tsananin rashin abinci da tsaro da ƙarancin samun damar ilimi da koyan sana’o’i da kuma harkokin kasuwancin da za su dogara da kansu.

Muhammad-Baba ya ce rayuwar akasarin mutanen arewacin ƙasar ya dogara ne ga ƙananan sana’oi, amma yanayin da ake ciki ya jefa da dama daga cikin su cikin halin ƙaƙanikayi da kuma rashin madogara, sakamakon manufofin tattalin arzikin da wannan gwamnatin ke ɗauka a matakin tarayya, ba tare da la’akari da irin uƙubar da yake jefa jama’a ba.

Ƙungiyar ta ce duk da yake ɗaukar irin waɗannan matakai na da matukar tasiri, amma kuma bai da ce ya yi illa ga mutanen da ake cewa ana yi domin su ba, saboda yanayin da ake ciki na iya hallaka wasu daga cikin su ta hanyar da ba za su iya cin moriyar gajiyar da za’a samu ba.

Muhammad-Baba ya ce sun buƙaci shugaban ƙasar da ya sake nazarin takunsa ta hanyar da zai dinga la’akari da rayuwar jama’a, tare da kuma sauraron ƙorafin jama’a domin gyara ga matakan da suke ɗauka waɗanda ke yiwa ƴan ƙasa illa.

ACF ta buƙaci ɗaukar matakan gaggawa ta hanyar aiwatar da manufofin kar-ta-kwana da kuma na dogon zango ta hanyar da za’a samarwa jama’a abinci, ciki hara da shigo da shi daga ƙasashen ƙetare, domin ragewa jama’a raɗaɗin halin da suke ciki.

Ƙungiyar wadda ta ce ta fahimci ƴan arewa ne kawai za su kare martabar yankin, ta buƙaci samun daidaito wajen raba mukamai da kuma gaggauta samo maslaha dangane da matsalar samar da wutar lantarki da talaucin da ya addabi jama’a da rashin ayyukan yi da kuma koma bayan da yankin ke fuskanta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Hukumar Kwastam ta Tantance Kusan Mutane 3,000 Yayin da Aikin Daukar Ma'aikata na 2025 ya KareMazauna Kauye Sun yi Murna Yayin da Sojoji Suka Dakile Harin Ta'addanci, Sun Kwato Shanu a SakkwatoFarashin Canji da Yawa ya ja wa Najeriya Asara Fiye da Tallafin Man Fetur – CardosoGwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato Makamai
X whatsapp