Atiku ya gargaɗi Tinubu kan yawan ciyo bashi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya ce yawaitar ciyo basussuka da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ke yi zai ƙara jefa tattalin arzikin Najeriya cikin ƙunci.

Atiku ya bayyana haka ne a wani rubuta da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce, “rahoton da bankin duniya ya fitar kwanan nan, wanda ke nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta uku da ta fi cin bashi daga hukumomin kuɗi na duniya abin damuwa ne.

Tsohon ɗantakarar na PDP ya kuma soki yadda majalisar dokoki ke amincewa da buƙatar ciyo basussukan, waɗanda a cewarsa suke ƙara jefa ƙasar cikin ƙangin bashi.

“Rahoton ya fito ne a daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ta aike da wani buƙatar sake ciyo wani bashin na naira triliyan 1.7 saboda cike giɓin kasafin kuɗin 2024. Abin da zai ƙara ɗaga hankali a game da bashin ma shi ne kasancewarar a kasafin kuɗin, an kasafta darajar dala ɗaya a kan naira 800, alhali yanzu dala ta kai naira 1,600.”

Ya ƙara da cewa Najeriya na ƙara nutsewa a cikin bashi, “sannan majalisar dokoki suna taimakawa. Tinubu ya bayyana a watan Yuli cewa hukumar tattara haraji da kwastam sun tara kuɗin shiga da ba a taɓa tarawa ba. To me ya sa ake cin bashin? akwai wani abu da suke ɓoyewa ƴan Najeriya.”

Atiku ya ƙara da cewa yawan cin bashin yana ƙara takurawa tattalin arzikin.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 9 hours 53 minutes 18 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 11 hours 34 minutes 43 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com