Sojojin Nijeriya sun sami nasarar kwato litar man fetur dubu 80 da aka sace a yankin Niger Delta.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da mukaddashin mataimakin daraktan yada labaran rundunar sojin ta 6 Laftanar kanal Danjuma Jonah Danjuma ya fitar a ranar lahadi, wadda ta ce dakarun sojojin shiyya ta 6 sun gudnar da wani sumame a daga rabar 18 zuwa 24 ga watan Nuwamban 2024.
a wani bangare na kakkabe masu yin zagon kasa ga tattalin arzikin yankin na Niger delta dake da arzikin man fetur.
Read Also:
sanarwar ta ce a jihar Bayelsa dakarun sun gudanar da sumame masu tarin yawa wanda ya suka sami nasarori, inda a karamar hukumar Ekeremor suka kama wani jingin ruwan katako dake dauke da lita sama da dubu 2 da dari 5 da aka sato.
haka kuma a garin Sangakubu da ke karamar hukumar Nembe, dakarun sun sami nasarar bankado matatar mai da bata garin ke aiki da ita ba bisa kaida ba, dakarun sun fadada ayyukan zuwa karamar kudancin Ijaw a yankin Tebidaba Creek, in da suka kame wani jirgin ruwan dauke wasu ma’adanai da aka sata.
yayin sumamen, dakarun sojojin sun lalata matatun mai 34 da ake gudanar da su ba bisa ka’idaba, gami da kama mutane 11 da ake zargi da satar mai da kananan jiragen ruwa 19.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 9 hours 54 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 11 hours 35 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com