Home General Ƙungiyar dattawan arewa ta yi watsi da Ƙudurin dokar sake fasalin haraji

Ƙungiyar dattawan arewa ta yi watsi da Ƙudurin dokar sake fasalin haraji

Kungiyar Dattawan Arewa ta NEF ta yi watsi da kudurin dokar sake fasalin haraji, tare da gargadin cewa yana barazana ga hadin kan kasa. Kungiyar ta soki yadda aka aiwatar da ita, inda ta yi zargin cewa an mayar da masu ruwa da tsaki ciki har da mambobin majalisar tattalin arzikin kasa a gefe yayin gudanar da aikin.

Shugaban kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, bayan taron kwamitin amintattu na karo na biyu na shekara-shekara, a Abuja ya bayyana haka.

Kungiyar ta yabawa kungiyar gwamnonin jihohin Arewa da kuma majalisar sarakunan arewacin Najeriya da suka nuna adawa da kudurin, inda suka bayyana matsayarsu a matsayin ‘yan kishin kasa, tare da yin kira ga ‘yan siyasar Arewa a majalisar dokokin kasar da su tofa albarkacin bakinsu.

Taron ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, dokar sake fasalin haraji an yi shi ne da nufin tursasawa yan kasar, kuma hakan barazana ce ga hadin kanmu da hadin kan kasa.

“Taron ya ci gaba da jawo hankulan mutane kan hanyar da ba ta dace ba da kuma yadda aka sanya dokar sake fasalin haraji a kan al’umma, ba tare da ba da damar shigar da masu ruwa da tsaki ba, kamar yadda ya sanya mambobin majalisar tattalin arzikin kasa cikin duhu.

“Majalisar, ta yi Allah-wadai da kakkausar murya, da irin hasarar murya da aka yi a kan wannan batu na yawan zababbun ’yan siyasa da suka fito daga yankin, tare da yi musu gargadi da kakkausar murya.

Kungiyar ta NEF ta bukaci ‘yan Arewa da su kara taka tsan-tsan wajen kare hakkinsu, musamman a lokacin zabe, ta kuma yi gargadin cewa kada su fada cikin magudin shugabanni marasa kishin kasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp