Hukumar Karɓar korafe-korafe ta Jihar Kano, ta gano wani babban rumbun ajiya da ake sauyawa shinkafar tallafi ta Gwamnatin Tarayya buhu domin sayarwa a unguwar Hotoro. Shinkafar wanda yawanta ya kai Tirela 23 na ɗauke da hoton Shugaba Bola Ahmad Tinubu wanda aka rubutu cewa shinkafar ba ta sayarwa ba ce. Ko dai a kwanakin baya, Al’ummar wata Unguwa sun daka wawa kan wata Shinkafa da aka zargi ita ma gwamnatin tarayya ta aike da ita jihar a rabawa talakawa domin rage radadi rayuwa.