Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzƙin Najeriya ta’annati, EFCC, ta ce ta kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a yau Talata.
Kafin hukumar ta tabbatar da kama shi rahotanni da dama na ambato cewa, tsohon gwamnan wanda ke fuskantar tuhumar almundahana, ya kai kansa ne ofishin hukumar da ke Abuja tare da rakiyar wasu lauyoyinsa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A wani hoton bidiyo na tashar talabijin ta Channels, kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da cewa hukumar tana tsare da tsohon gwamnan na Kogi.
Taƙaddama ta kasance tsakanin EFCC da tsohon gwamnan, bayan da hukumar ta ayyana nemansa a watan Afirilu, bayan ya ƙi amsa gayyatar da ta sha aika masa tare da nuna tirjiya kan duk wani yunƙuri na kama shi, wanda hakan ya sa ya shiga kulli-kurciya da hukumar.












