A yau Laraba ne shugaban ƙasa Bola Tinubu zai tafi ƙasar Faransa domin ziyarar aiki.
A wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ne ya gayyaci shugaban na Najeriya.
Read Also:
Onanuga ya ce ziyarar ta kwana uku ce, kuma za ta mayar da hankali ne, “kan inganta alaƙar tattalin arziki da dimokuraɗiyya da noma da tsaro da ilimi da kiwon lafiya da samar da aikin yi ga matasa da sauran abubuwa muhimmai.”
Sanarwa ta ƙara da cewa Tinubu zai yi tafiyar ce tare da matarsa, Sanata Oluremi Tinubu, inda shugaban na Faransa ta matarsa za su tarbe su.
Haka kuma Oluremi Tinubu da uwargidan shugaban ƙasar ta Faransa, Brigitte Macron za su gana game da shirin uwargidan shugaban Najeriya na Renewed Hope Initiative na inganta rayuwar matasa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 18 hours 15 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 19 hours 56 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com