Home General Zamu samar da cibiyar hada kayan aikin CNG a Jihar Kogi –...

Zamu samar da cibiyar hada kayan aikin CNG a Jihar Kogi – FG

Najeriya ta samu gagarumin ci gaba wajen haɓaka cibiyoyin sauya motoci zuwa na amfani da gas ɗin CNG, daga bakwai a 2023 zuwa 158 a 2024 – ƙaruwar da ta kai kaso 2000%.

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gas ɗin CNG, Injiniya Michael Oluwagbemi, ya bayyana hakan a taron Nigerian Content karo na 13 a jihar Bayelsa.

Ya bayyana shirin faɗaɗa cibiyoyin zuwa sama da 1,000 don biyan buƙatun masu amfani da ababen hawa.

“Manufar ita ce sauya motoci daga amfani da man fetur zuwa gas ɗin CNG, don ƙirƙirar kasuwar da za ta tallafa wa tashoshin sayar da gas,” in ji shi.

Ya bayyana cewa farashin sauya mota ɗaya yana kusan Naira miliyan ɗaya, kuma akwai damar kasuwa ta Naira tiriliyan 5 don sauya motoci miliyan biyar a Najeriya.

An kuma shirya kafa cibiyar ƙera kayan aikin CNG a Ajaokuta, jihar Kogi.

Shirin ya haɗa da gina ƙarfin aiki, tare da kafa cibiyoyin bayar da horo 1,000 don tabbatar da gyaran motoci a cikin gida.

An fara amfani da kayan gas masu ɗaukar nauyi da aka samo daga fasahar Indiya don magance matsalolin gine-gine.

Oluwagbemi ya jaddada haɗin kai tare da hukumomi don tabbatar da shigar da gas ɗin CNG cikin tsarin makamashi na ƙasa.

“Muna gina tsarin tattalin arziki da zai rage dogaro da man fetur,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Muna da filin hekta 10 kuma muna da niyyar ƙera manyan abubuwan kayan aikin a cikin gida ta hanyar nazarin fasaha,”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp