Home AFIRKA Ƴan bindiga sun hallaka fararen hula 21 a yammacin Jamhuriya Nijar

Ƴan bindiga sun hallaka fararen hula 21 a yammacin Jamhuriya Nijar

Akalla fararen hula 21 ƴan bindiga suka kashe a ranar asabar da ta wuce yayin wani hari da suka kai kan wata mota sufurin fasanja a yankin Tera da ke Jihar Tillabery  a yammacin Jamhuriya Nijar, kamar yadda gidan talabijin ɗin ƙasar ya sanar.

A rahoton mako-mako da ma’aikatar tsaron ƙasar ta saba fitarwa, gwamnatin ta ce an kai harin ne da misalin  ƙarfe 5 na yammacin rana  asabar daidai  lokacin da kasuwar kauyen ke tsaka da ci,  abunda ya sa aka samu asarar rayukan fararen hula da dama.

Rahoton ya ƙara da cewa ko a ranar Juma’a da ta gabata sai da dakarun ƙasar biyu suka mutu  bayan da ayirin motocinsu ya taka wani abun fashewa da aka dana a kauyen Tiyawa duk dai a Jihar ta Tillabery.

Da ya ke jagorantar  zana’izar waɗanda suka mutu a harin, gwamnan Jihar Tillabery Kanal Maina Bukar ya jajintawa iyalansu da sunan gwamnati, tareda fatan samun lafiya ga waɗanda sukaji rauni.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da dakarun ƙasar ke ƙara kaimi wajan fatattakar ƴan bindiga da ke addabar jama’a a wanan yankin da yaraba iyaka da ƙasashen Mali da Burkina.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp